News
Toshon Akanta Janar Ya Nemi Ƙarin Lokaci Don Maida Kuɗin Da Ya Sace
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Tsohon muƙaddashin Akanta Janar na Najeriya, Anamekwe Nwabuoku, ya roƙi mai shari’a James Omotoso na babbar kotun ƙasar da ke Abuja kan ya ƙara masa lokaci domin ya kammala mai da kuɗaɗen al’umma da ake zargin su yi rub da ciki akai, shi da Felix Nweke.
Tun da farko hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da su a gaban kuliya, bisa wasu zarge-zarge da su ka shafi almundahanar kuɗaɗe.
Nwabuoku da Felix Nweke dai, suna fuskantar tuhume-tuhume 11 game da almundahanar kuɗaɗen da suka Naira Biliyan da miliyan ɗari 6.
Ana kyautata zaton Nwabuoku ya aikata laifin ne yayin da ya rike muƙamin Daraktan kuɗi a ma’aikatar tsaron ƙasar tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.
Yayin da shi kuma wanda ake tuhuma na biyu Felix Nweke, ya taimaka wajen kitsa kitimurmurar, kwashe kuɗaɗen, tare da yin kasha-mu-raba.
A ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2022 ne, tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, ya naɗa Nwabouku a matsayin muƙaddashin babban akanta na ƙasar, ƴan kwanaki bayan da aka dakatar da tsohon babban akanta Ahmad Idris, bisa zargin yin hafzi da Naira Biliyan 80.
Fri
