Connect with us

News

Da Dumi Dumi: Kotun Koli Ta Hana Gwamnonin Rike Kudaden kananan hukumomi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kotun koli ta yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnonin jihohi 36 kan cin gashin kan kananan hukumomi.

Advertisement

Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito cewa A cikin karar, Babban Lauyan Gwamatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya nemi cikakken ‘yancin cin gashin kai da kuma raba kudade kai tsaye ga kananan hukumomi 774 na kasar nan.

Toshon Akanta Janar Ya Nemi Ƙarin Lokaci Don Maida Kuɗin Da Ya Sace

Ya bukaci kotun kolin da ta yi amfani da sashe na 1, 4, 5, 7 da 14 na kundin tsarin mulkin kasar domin bayyana cewa gwamnoni da majalisun jihohi suna da hakkin tabbatar da tsarin dimokuradiyya a mataki na uku.

Advertisement

A hukuncin da ta yanke wanda mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun kolin ta bayyana cewa ba bisa ka’ida ba ne gwamnoni su rike kudaden da ake bukata na kananan hukumomi .

Mai shari’a Agim ya ce kin amincewar da gwamnatin jihar ta yi na cin gashin kan kananan hukumomi ya shafe sama da shekaru ashirin.

Advertisement

A cewarsa, tun daga lokacin ne kananan hukumomi suka daina karbar kudaden da aka tanadar musu daga gwamnonin jihohin da ke aiki a madadinsu.

Yayin da yake lura da cewa ya kamata kananan hukumomi 774 na kasar su gudanar da kudaden su da kansu, ya yi watsi da matakin farko na wadanda ake kara (gwamnonin jihohi).

Advertisement

Mai shari’a Agim ya ce AGF na da ‘yancin kafa wannan kara da kuma kare kundin tsarin mulki.

Don haka, kotun kolin ta bayar da umarnin a biya su kudaden kananan hukumomi daga asusun tarayya kai tsaye daga yanzu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending