News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Sake Maka Ganduje A Kotu Kan Wasu Sabbin Zarge-Zarge
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Kano a ranar Talata ta shigar da sabon kara kan tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Ganduje.
A cikin takardar karar mai lamba K/143c/24, gwamnatin jihar ta zargi Ganduje da tsohon Kwamishinan Shari’a, Musa Lawan, da hada baki wajen aikata laifi da kuma almubazzaranci wanda ya saba wa Sashe na 308 kuma za a hukunta su karkashin Sashe na 309 na Kundin laifuka da hukunce hukuncensu a Penal Code (wanda aka gyara) CAP 105, Vol. 2, a Dokokin Jihar Kano da Najeriya.
Laifin, in ji gwamnatin jihar, ya sabawa doka kuma za a hukunta su a karkashin Sashe na 97 da Sashe na 315.
Gwamnatin jihar ta zargi Ganduje da Lawan da yin amfani da ofis ta hanyar da bata dace ba. A cikin takardar karar, gwamnatin jihar ta ce tana da niyyar gabatar da shaidu hudu.
Kawo yanzu dai ba a sanya ranar da za a gurfanar da su a gaban kotu ba.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Afrilu, gwamnatin jihar ta shigar da kara Ganduje, matar sa, Hafsat Umar, da wasu mutane shida a gaban babbar kotun jihar Kano.
Mutane shida sun hada da dan Ganduje, Umar Abdullahi Umar, Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad, Kamfanin Lamash Properties Ltd., Safari Textiles Ltd., da Lesage General Enterprises.
KARANTA: Dalilin Da Ya Sa Ban Je Kotu Ba Bayan Ganduje Ya Tube Ni – Sarki Sanusi II
Kotun ta sanya ranar yanke hukunci kan ƙorafin farko da lauyan su, Nuraini Jimoh SAN, ya shigar game da karar da aka shigar kan abokan huldar sa.
Lokacin da aka ci gaba da sauraren shari’ar, Mai Shari’a Amina Aliyu ta bayyana damuwarta cewa wadanda ake kara sun kasa bayyana a kotu duk da an kai musu takardar shaidar sammaci ta hanyar wasu kafofi.
Lauyan masu gabatar da kara karkashin jagorancin Adeola Adediyo, SAN, ya bukaci kotun ta sanya umarnin kama Ganduje, matar sa da wasu mutane
