Connect with us

News

Yan Ta’adda Sun Yi Garkuwa Da Mutane 150 Tare Da Kashe 4 A  Zamfara

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rahotannin daga Jaridar PRNigeria na nuni da cewa a jihar Zamfara wasu ‘yan taádda masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun yi garkuwa da mutane 150 cikin su har da yara kanana a kauyen Dan isa dake karamar hukumar kaura Namoda dake jihar.

Advertisement

harin ya faru ne makwanni kadan bayan da ýan bindigara suka saki mutune 46 mazauna garin Dogon kade da suka saka bayan an biya kudin fansa naira miliyan 21.

Gwamnatin Jihar Kano Ta Sake Maka Ganduje A Kotu Kan Wasu Sabbin Zarge-Zarge

dan isa dai gari ne dake da nisan kilomita 14 zuwa birnin jihar wato gusua.

Advertisement

 

jaridar Emergency Digest ta ruwaito wani mazaunin garin da aka yi garkuwa da matarsa da dan Sa na tabbatar da aukuwar lamarin.

Advertisement

‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane 150 tare da kashe 4 a jihar Zamfara

mutumin wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce ‘yan ta’addan sun tasamma garin ne kan babura kusan 150, kowannen su dauke da mutane uku, inda suka fara harbi a iska, abinda ya sa wasu cikin al’umma guduwa domin neman tsira.

Advertisement

“Matata, Na’imah da Da na dan watanni shida a duniya, Sudais, na cikin wadanda ”Yan ta’addan suka yi garkuwa da su, sai matar kanina, Aisha, da yaron ta dan watannin takwas, mata da yawa da kananan yara ýan binidgar sukayi garkuwa da su,” a cewar sa.

wani mzaunin garin Muhammad Auwal (ba sunansa na gaskiya kenan ba), ya ambaci cewa Hajiya Rakiya, matar Wamban Dan Isa, Alhaji Bello Halilu, da wasu mata ‘yan taáddan suka raunata a gidan Alhaji Halilu.

Advertisement

Aminu Bello Dan isa, wani mazaunin garin ya ce gungun ‘yan ta’addan dake karkashin dan bindiga Alhaji Shehu Bagiwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending