News
Ta Yiwu Zaɓen Ƙananan Hukumomi Zai Koma Hannun INEC —Majalisar Wakilai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Biyo bayan hukuncin kotun ƙolin a ranar Alhamis da ta gabata, ta yiyu yan majalisa su yi wa kundin tsarin mulkin mu kwaskwarima yadda zaɓen ƙananan hukumomi zai dawo hannun INEC.
Yayin wani taron manema labarai, Sanata Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta Kudu yace, za su tabbatar gwamnoni sun yi biyayya ga hukuncin kotun. Sannan suma za suyi iya ƙoƙarin wajen yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don ganin hakan ya tabbata.
DA DUMI DUMI : Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Kafa Masarautu Masu Daraja Ta Biyu
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanata dake wakiltar Delta ta kudu, ya bayyana cewa dole su yi wa kundin tsarin mulkin gyara domin a ba Hukumar INEC ragamar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin.
Yace dole a ba mutane dama su rinƙa zaɓen wanda suke so. Ba kamar abun da ke faruwa ba yanzu. Ya bayyana zaɓen ƙananan hukumomi da akayi a Delta satin da ya gabata a matsayin wasan kwaikwayo ne kawai.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
