News
Dun bulki kwamanda: babu wani Jami,in Hukumar da ya isa ya hanani yawo da bindinga
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen dan siyasar Baka da yayi shura a kafafen yada labarai wato alhaji abdulmajid dan bulki kwamanda yace babu wani jamian Hukuma da ya isa ya hanani yawo da bindinga
Kwamanda ya fadi hakanne Cikin wata hira da akayi dashi a wata kafar yada labarai ta radio inda yace a yanzu duk wata tafiya idan zanyi tom babu shakka sai yayi yawo da bindinga
A cewar sa kodan irin wulakanci da wadannan jami an da gwamnan uba sani ya turosu sukaimin akan hanyata ta Kaduna zuwa Abuja sainayi amfani da ita
Yace nafi karfin shekaru 25 da license din bindinga adan haka Zan Kara sabinta Shi kodan Karin wasu bindigogin
Yan ta,adda ma Wadanda basuda lisisin rike bindinga Suna amfani AK47 kuma Suna yawo da ita a kowanne lokaci Kuma duk lokacin da suke so ballatana ni da nake da lasisi Kuma nake gwagwarmaya akan kare hakkokin dimucradiyya
Dan bulkin kwamanda ya Kuma ce tabbas gwamnan Jahar Kaduna uba sani yanada sa hannu wajen irin rashin mutuncin da wasu daga cikin jamia sukai masa
daga karshe Ya kumace jinjinawa al,ummar Jahar Kaduna inda yace tabbas sun fara sanin Kansu wajen ganin sun sami sauki akan sha,anin mulkin dumukradiyya
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
