Connect with us

News

Mayakan Boko Haram 50 Sun Mika Wuya Ga Dakarun Sojoji A Borno

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dakarun sojojin kasan Nijeriya sun sami nasarar kama kwamandan kungiyar Boko, mai kai musu kaya da kuma wadanda suke hada baki, gami da mayakan kungiyar da suka mika wuya da iyalansu.

Advertisement

PRNIGERIAN ta ruwaito cewa Haka kuma dakarun rundunar sun sami nasarar kwato wadanda mayakan kungiyar suka yi garkuwa da su a mabambanta maboyar su, haka kuma dakarun sun sami nasarar kwato wasu kayyaki da bata gari suka sace a yayin gudanar da zanga-zangar luma a kasar.

Tunibu ya naɗa Masari a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta ilimin manyan makarantu – Tetfund

 

Advertisement

Rundunar sojojin tace a ranar 4 ga watan Agusta, 2024 bisa aiki da wasu bayanan sirri dake yi ta sami nasarar kama wasu kwamandojin mayakan kungiyar boko haram a jihar Borno, wadanda ke yunkurin kutsawa sansanin ‘yan gudun hijira dake Damasak a karamar hukumar Mobbar.

Wadanda ake zargin da suka hadar da Bana Yamode da babagana Usman, wanda suka yi ikirarin sun je sansanin ne domin ziyartar iyalen su, wadanda tun da fari dama su sukayi jagoranci kai hari a yankin.

Advertisement

Haka kuma dakarun sun sami nasara kama wadanda ake zargi da safarar kayayyaki guda biyu Mallam Mustapha Isma’il mai shekaru 49 da kuma Abdulmudalibi Haruna mai shekaru 30, tare da ceto wasu mutum biyu a yayin sumamen.

Haka kuma mayakan boko haram 50 da iyalansu sun mika wuya ga rundunar a kananan hukumomin Bama, Gwoza da Dikwa, wannan dai na zuwa ne bisa yunkurin dakarun sojojin na kakkabe mayakan na boko haram.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending