Sports
Ɗan Wasan Ƙasar Portugal Pepe Ya Sanar Da Ritaya Daga Ƙwallon Ƙafa

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shaharren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa Portugal Pepe ya sanar da ritayar shi daga wasan ƙwallon ƙafa.
Pepe ɗan shekara 41, yayi wannan sanarwar ne ta hanyar wallafa bidiyo daga shafinsa na sada zumunta.
Za A Rufe Gidajen Burodi Saboda Tsadar Fulawa Bayan Zanga-Zanga A Kano
Pepe in bamu manta ba, gogaggen ɗan wasan baya ne. Ya fara taka leda a ƙungiyar Maritino inda daga nan ya tafi ƙungiyar kwallon ƙafa da Real Madrid inda ya shafe shekaru 10 yana taka leda.
Ya samu damar lashe kofuna kamar kofin zakarun turai na Champions League har guda uku, yayi nasara cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2016.
Pepe ya kasance ɗan wasa mafi tsufa da ya buga gasar Nahiyar Turai. Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal ya bayyana shi a matsayin gwarzo da za a jima ba a samu irin shi ba.