News
Sanatan Kano Ya Bayyana Yadda Sanatoci Suke Samun Naira Miliyan 21 A Duk Wata
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, ya bayyana cewa yana samun jimillar Naira miliyan 21 a duk wata a matsayin albashi da alawus, biyo bayan karin albashi da aka yi a baya-bayan nan.
Sanatan ya bayyana hakan ne a wata hira da sashen Hausa na BBC a safiyar Laraba.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Fasinjoji Da Dama A Hanyar Gusau Zuwa Funtua
Sanata Sumaila ya fayyace cewa albashin sa a hukumance bai kai Naira miliyan daya ba.
Sai dai ya bayyana cewa kowane Sanata yana karbar karin Naira miliyan 21 a duk wata a matsayin kudin gudanar da aiki, wanda ya bambanta da albashin su na hukuma.
“Kudin da ake karba na albashi a wata bai kai Naira miliyan daya ba, idan an yi yanke-yanke ya kan dawo kamar Naira dubu dari shida da dan wani abu a matsayin albashi,” in ji Sanata Sumaila.
Idan aka yi la’akari da karuwar da aka samu, a Majalisar Dattawa, kowane Sanata na samun Naira miliyan 21 a duk wata a matsayin kudin tafiyar da aikin.
Wannan fallasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce game da kudaden da ‘yan majalisar tarayya ke samu a Najeriya, musamman a halin da ake ciki na kalubalen tattalin arziki.
Hukumar tattara kudaden shiga da kasafi da kasafin kudi (RMAFC) a baya ta bayar da rahoton cewa, adadin albashi da alawus-alawus din kowane sanata a duk wata ya kai N1,063,860, wanda ya hada da ainihin albashin N168,866.70 da alawus-alawus iri-iri na gyaran ababen hawa, mataimaka, ma’aikatan gida. nishadi, kayan aiki, yan jaridu, tufafi, gyaran gida, da kuma kuɗaɗen mazaɓa.
