Connect with us

News

Jigawa: Ambaliyar Ruwa Tayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 16 Tare Lalata Gidaje 3,936 

Published

on

Jigawa Ambaliyar Ruwa Tayu Sanadiyar Mutuwar Mutane 16 Tare Lalata Gidaje 3,936 

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), ta tabbatar da mutuwar mutane 16 tare da lalata gidaje 3,936 sakamakon ambaliyar ruwa.

Advertisement

Ya kuma ce ambaliya ta kuma mamaye kadada 2,744 na gonaki biyo bayan mamakon ruwan sama tun da aka fara daminar shekarar 2024.

Hukumar UNICEF tace rashin abinci mai gina jiki ya yiwa kashi 57 na yaran Kano illa

Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Haruna Mariga, wanda ya bayyana hakan a Dutse ranar Laraba, ya ce bala’in ya shafi kananan hukumomi 10 na jihar.

Advertisement

Mairiga ya ce mutanen sun mutu ne sakamakon rugujewar gini, nutsewa da kwalekwale.

Ya ce bala’in ya yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da mutane 3,936 da suka rasa matsugunansu yayin da hekta 2,744 na gonaki suka nutse,” in ji shi, ya kara da cewa lamarin na iya kara kamari saboda yawan ruwan sama da ake sa ran zai yi.

Advertisement

Mairiga ya ce hukumar ta samar da matsuguni na wucin gadi tare da raba kayan agaji ga ‘yan gudun hijirar domin rage musu radadi.

 

Advertisement

 

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending