Connect with us

News

Yadda Wasu Ƴan Uwa Biyu Suka Binne Ƙaramin Ƙanin Su Dan Shekara 16 Da Ransa A Zariya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

A wani lamari mai ban al’ajabi da tayar da hankali, an sami rahoto yadda wasu ƴan uwa biyu suka binne ƙaramin Ƙanin su Dan shekara 16 da ransa mai suna Abubakar sakamakon ɓatan waya a garin Zariya na jihar Kaduna.

Sai dai Ƴan sanda sun yi nasarar kama waɗanda suka aikata laifin, ɗaya mai shekaru 22 da kuma 18, bayan da wani mutum ya hangi kan Abubakar yana reto a rami cikin wani kango.

Zanga Zanga: An Sace Muhimman Takardun Tuhume Tuhumen Da Ake Yi Wa Ganduje – Gwamnan Kano

A cewar shaidun gani da ido, ‘yan’uwan sun samu rashin jituwa dalilin wata waya da ta bata a Abuja, inda suke aiki.

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa ‘yan uwan sun biyo Abubakar har Zariya inda suka binne shi da rai a matsayin azabtarwa.

Advertisement

Kwamishinan ma’aikatar jin dadin jama’a da ci gaban jama’a na jihar Kaduna, Rabi Salisu ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba.

“Sai da suka ɗauke yaron, sannan suka kulle bakinsa. Sai suka binne shi a cikin rami, kansa ne kawai a waje. Ban taba ganin an binne wani da rai a fili ba in ba a fim ba. Yaron mai suna Abubakar dan shekara 16 ‘yan uwansa sun yi masa wannan azaba ne saboda bacewar wayar.

“Sun tona rami, inda suka daure hannayensa bayan sunrufe bakinsa. Sannan Suka binne shi, kansa kawai suka bari a waje a lulluɓe da tsumma a cikin wani kango kusa da wata gona. Wani bawan Allah ne da ya ji yaron yana tari wanda hakan ya jawo hankali wasu manoma har suka ceto yaron, kamar yadda faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta ke kunshe.

“Wadanda suka aikata laifin da mai shekara 22 da dan uwansa, dan shekara 18 ne ƴan sanda sun yi nasarar kama su.Za mu je kotu bayan bincikensu. Gwamnati ba za ta dauki hakan da wasa ba, wajen kare hakkin yara da sauran wadanda ake tauye hakkinsu a jihar Kaduna,” inji Rabi Salisu

Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Mansir Hassan, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ya ce wadanda ake zargin suna tsare kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

Hassan ya ce masu laifin sun amsa laifin su.

Advertisement

A halin da ake ciki kuma, a cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da ci gaban jama’a ta jihar, ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa ta dauki kwakkwaran mataki bayan afkuwar lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wanda aka binne, Abubakar Aliyu, ya tsallake rijiya da baya, kuma tuni aka kubutar da shi. ‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargin.

“Jami’in jin dadin jama’a da ke Zariya ya ziyarci yankin da lamarin ya afku domin duba halin da ake ciki tare da bayar da tallafin da ya dace. Ma’aikatar ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci kuma za su ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin.

“Kuma Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika da kakkausar murya tare da jaddada kudirinta na kare hakki da walwalar ƴan kasa musamman kananan yara.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending