Connect with us

News

Zanga Zanga: An Sace Muhimman Takardun Tuhume Tuhumen Da Ake Yi Wa Ganduje – Gwamnan Kano

Published

on

L R Abba Kabiru Yusuf and Abdullahi Umar Ganduje

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin jihar kano ta ce masu zanga-zangar sun sace Muhimman takardun da ake ake tuhumar tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da Kuma wasu daga cikin mukarraban gwamnatinsa .

Advertisement

Idan za a iya tunawa  a watannin bayan gwamnatin jihar kano ta maka Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa a gaban babbar kotun jihar Kano bisa wasu zarge-zarge na almundahanar kudade.

Zasu Gurfanar Da Wasu Daga Cikin Yan Kasuwar Singa A Kotu Akan  Zargin Karin Fashin Kayayyakin Masarufi  —Muhyi Magaji

” Wasu makiya jihar kano sun dauki nauyin wasu bata gari da suka fake da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da aka yi a Nigeria, inda suka shiga cikin babbar kotun jihar Kano kuma suka sace Muhimman takardun tuhumar da muke yiwa tsohon gwamnan jihar kano da mukarrabansa”.

Advertisement

Gwamna jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci harabar babbar kotun jihar dake sakatariyar Audu Bako.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce gwamnan ya nuna damuwa kan abun da ya faru na lalata dukiyoyi masu tarin yawa a kotun, tare da sace muhimman takardun tuhumar da ake yiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement

Sanarwar ta ce masu zanga-zangar sun lalata kaya na sama da naira biliyan 1, wadanda suka hadar da kayan Ofisoshi da sauran kayiyakin amfani na Ofishin babbar mai Shari’a ta jihar Kano da harabar kayan kotun.

“Abin takaici ne matuka yadda makiya jihar Kano suka dauki hayar wasu bata gari suka lalata daya daga cikin gine-ginen al’umma mai dimbin tarihi da nufin kawar da zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa da mataimaka.”

Advertisement

Sanarwar ta kara da cewa barayin sun lalata kusan dukkanin sassan babban kotun da suka hada da ofishin Alkalin Alkalan jihar da hasarar sama da naira biliyan daya ta hanyar sace kayan ofis, lalata ofisoshi, kona motoci da sauran kayan aiki masu muhimmanci ga aikin. na Shari’a .

Alhaji Abba Kabir ya yi kira ga matasa a jihar da su daina bari ana amfani da su wajen yin tashe-tashen hankula, sai dai su maida hankali wajen neman sana’o’in hannu domin samun kyakkyawar makoma tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.

Advertisement

Gwamnan ya bada tabbacin cewa Jiduciary a matsayin fata na karshe na talaka dole ne a kiyaye shi ko ta halin kaka, don haka ya ba da umarnin a gaggauta gyara ginin tare da samar da isasshen tsaro domin tabbatar da adalci.

Ya kuma jajantawa babban alkalin kotun, Dije Abdu Aboki da daukacin yan bangaren shari’a kan wannan munmunan lamari .

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending