Connect with us

News

Kotu Ta Tisa Ƙeyar Wani Alƙalin Bogi Zuwa Gidan Yari A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wata kotun Musulunci ta tisa ƙeyar wani alƙalin bogi zuwa gidan yari a Jihar Kano.

Advertisement

Dubun alƙalin bogin ta cika ne bayan da ya gabatar da kansa a matsayin alkali daga Jihar Jigawa a gaban Kotun Musulunci da ke unguwar Kurma, Ƙaramar Hukumar Fagge.

Mutum 2 Sun Mutu A Rushewar Bene Mai Hawa Biyu A Kano

Asirin alƙalin bogin ya tonu ne a lokacin da ya je kotun neman belin wasu mutane biyu wadanda ake zargi da laifin damfara da cin amana.

Advertisement

Kotun ta amince da ba shi belin mutanen ne a bisa sharaɗin sai ya kai jami’an kotu gidansa, amma nan take ya ƙi amincewa.

Da aka tsananta bincike daga baya sai aka gano cewa ungulu da kan zabi ya yi, ma’aikacin shari’a ne, amma bai taɓa zama alkali ba.

Advertisement

A lokacin da aka gurfanar da shi, ya amsa laifinsa, sannan ya roki alkalin ya yi masa sassauci.

Khadi Umar Lawan Abubakar ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari zuwa ranar 23 ga watan Satumba, 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending