News
Hukumar DSS ta saki Omoyele Sowore Shugaban Jaridar Sahara Reporters
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Hukumar jami,an tsaro ta DSS ta saki Omoyele Sowore mai rajin kare hakkin dan Adam mamallakin Jaridar Sahara Reporters kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (ACC) a zabukan 2019 da 2023.
Da safiyar yau Lahadi ne Sowore ya wallafa cewar jami’an DSS sun cafke shi a yayin da yake shigowa Najeriya amma daga bisani jami’an sun sallame shi kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.
Haka kuma hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta dawomashi da lasisinsa na Kasa da Kasa fasfo da aka kamashi dashi a filin jirgin saman dake Legas.
Tun da safiyar yau Lahadin ne jami’an hukumar shige da fice ta Kasa suka tsare Sowore a filin jirgin bisa zargin da hukumar takeye akan da hannunsa a tada zaune tsaya a lokacin yin zanga -zangar matsin rayuwa.
Yanzu an sake ni. An dawo mini da fasfo na da komai,” in ji Sowore yayin da yake tabbatar da sakin sa.
Jirginsa dashi ya Iyalansa ya taso daga filin jirgin saman Washington Dulles da misalin karfe 6.14 EDT ya isa Legas da misalin karfe 9.43.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
