News
Lalacewar Hanya: Ya Kamata Gwamnatin Jihar Kano Ta Tallafawa Alummar Unguwar Dan Dishe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An bukacin Gwamnan kano Abba kabir Yusuf daya Tallafawa alummar unguwar Titin Dan dishe makarantar boko tudun Fulani bisa halin da yankin ke ciki a halin yanzu
Wani mazaunin yankin Auwal Lawan shine ya bayyana hakan a zantawar sa da Jaridar kadaura24 a jihar Kano
Yana Mai cewar Tabbas yana yin da yanikin ke ciki babbbar barazana ce ga mazauna yankin musan manma yara da mata da kuma Dattawa.
Auwal lawan ya kuma ce yankin nada Alumma da dama da suke rayuwa amma rashin kyawun hanyar yasa mazauna yankin na fadawa cikin wani hali.
A Dan haka ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta tallafa musu a kan lamarin kamar yadda yayi Alkawari a baya
Advertisements
