News
Aƙalla Mutum 40 Ne Masu Mauludi Suka Rasu Sanadiyyar Haɗarin Mota
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Aƙalla mutum 40 ne masu Mauludi suka rasu da yammacin ranar Lahadi, sakamakon wani haɗari inda wata babbar motar kaya ta hau kan wata mota ƙirar J5 ɗauke da mutum fiye da 70.
Wani wanda ɗaya ne daga masu shirya Mauludin ya shaida wa BBC cewa “daga garin Kwandari za su zo nan Saminaka a daidai Lere kan kwana wata babbar mota ta hau kan motarsu.
An ce wani mai babur ne ya gifta wa direban babbar motar inda shi kuma mai babbar motar ya kauce masa abin da ya sa ya hau kan motar masu Mauludin.”
Mali, Burkina Faso Da Nijar Za Su Ƙaddamar Da Fasfo Ƙarkashin Sabuwar Ƙungiyar Ƙawancensu
Bayanan sun ce aƙalla mutum 30 ne suke a asibiti inda suke samun kulawa.
Wani wanda shi ne mutumin da ya ɗauki alƙaluma bayan haɗarin ya ce “waɗanda suka mutu su 41 ne mata guda 19 da ƙananan yara 10 da sauran mutane musamman tsaffi kusan 11 sai kuma masu rauni fiye da 30.”
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
-
News1 day ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
