News
Kwamitin SHCSS Ya Horar Da Ma’aikatan Lafiya Kan Yadda Ake Ƙiyasin Magunguna
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A kokarinsa na ci gaba da tabbatar da tsarin samar da magunguna mai ƙarfi kuma mai ɗorewa a dukkan asibitoci mallakin Kanona, Kwamitin Tabbatar da Samar da Magunguna mai Ɗorewa (SHCSSC) ya shirya taron kwanaki 3 ga ma’aikatan bayar da magunguna asibitoci daga wasu ƙanana da manyan asibitocin gwamnatin jihar.
Horon dai ya samu cikakken tallafi daga Shirin Kula da Lafiyar Jiki da kawar da Cutar Amai da Gudawa na Ƙasar Kanada ta ƙarƙashin Shirin Cigaban Ilimi, Kawar da Talauci da Ƙamfar Abinci (FAcE-PaM)
Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayar Da Umarnin Rufe Hanyar Buk Road Ranar Alhamis
Yunƙurin bada horon dai an yi shi ne don fahimtar da mahalarta taron rawar da dabarun samar da magunguna ke takawa wajen wanzauwa magunguna a asibitoci, da dabarun da ake amfani da su waje zaɓa da yi wa magunguna ƙiyasi da kuma hanyoyin da ake bi wajen sayo da kuma karɓar magunguna a asibitoci.
A jawabinsa na buɗe taron, shugaban Kwamitin na SHCSS kuma daraktan kula da samar da magunguna na Ma’aikatar Lafiya, Pharm. Kamilu Mudi Salisu ya jaddada mahimmancin sanin ƙiyasin magunguna a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙai na ayyukan samar da magunguna, inda ya ƙara jaddada cewa idan aka tafi da tsarin yadda ya kamata za a samu magunguna masu inganci kuma akan farashi mai ɗorewa.
Pharm. Kamilu Ya kuma buƙaci mahalarta taron da su saurari dukkan maƙalolin da za a gabatar tare da yin tambayoyi kan duk wani abu da ya shige musu duhu, yana mai cewa hakan zai taimaka musu wajen fahimtar ilimin da za a ba su domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a asibitoci.
Sannan ya ƙara jaddada ƙudirin kwamitin SHCSS na tabbatar da lalacewar magunguna ba, wanda hakan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya aka shirya taron bitar baya ga samar da magunguna a dukkan asibitocin jihar.
Shugaban ya yaba wa Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake bai wa ɓangaren lafiya na jihar muhimmancin gaske, wanda ya haifar da gagarumar nasara a cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin Dakta Abubakar Labaran Yusuf na yadda yake jagorantar sake sauya fasalin tsarin ta hanyar kawo sabbin dabaru da tunane-tunane ƙari ayyuka da shirye-shirye da ya tarar da nufin sabunta tsarin.
Pharm Kamilu ya kuma jinjina wa Shirin Kula da Lafiyar Jiki da kawar da Cutar Amai da Gudawa na Ƙasar Kanada da Shirin Cigaban Ilimi, Kawar da Talauci da Ƙamfar Abinci (FAcE-PaM) bisa gudunmawar da suke bai wa jihar Kano kan inganta ayyukan samar da magunguna, yana mai ba su tabbacin ci gaba da gudanar da alaƙar aiki a kowane lokaci.
