News
Kungiyar Vision Spring Da Tallafin M’G’E Medical Store Sun Yiwa Masu Fama Da Larurar Ido Gwaji Kyauta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Vision Spring dake Karkashin kulawar EHA CLINIC tare da tallafin M G E Medical Store sunyiwa Al’umma masu larurar gani sama da Mutane 300 gwajin Ido Kyauta tare da basu magangunan da zasu ruga amfani dasu dan magan ce matsalolinsu.
Kungiyar tayi wannan taron gwajin Idon ne a ranar Alhamis a harabar Babban Shagon MGE dake Unguwar Tudun Yola Gate Five 5.
Badaƙalar Filaye: Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Ma’aikatan Kotu A Kano
Shugaban M’G’E Medical Store Yunusa Musa Rabiu dake da Kwarewa a fannin hada magunguna da Kuma sanin cututtuka masu yaduwa ya ce kungiyar Vision Spring tayi wannan gwajin Idon Kyauta ne domin baiwa Al’umma masu Larurar damar fadin abinda yake damunsu musamman ma Mutanen da Shekarunsu suka haura 35.
Sannan kuma masanin ya Kara da cewa bayan sunyi gwaji kyauta suna duba irin matsalar da mutum yake da ita sannan su dorashi akan magani.
Bayan kwajin kyauta kuma kungiyar Vision Spring tayi ragin kaso Tamanin 80 cikin Dari 100 ga wadan gwajin ya nuna Gilashi za’abasu ko kuma magani.
Yunusa Musa Rabiu ya ce wannan shine Karan farko da Vision Spring ta duba masu matsalar gani a Unguwar ta Tudun Yola kuma nan bada jimawaba kungiyar zata dawo domin sake duba wasu masu neman lafiya.
A nasa jawabin shima Mai Unguwar Tudun Yola Malan Kabir Shehu Abdullahi ya nuna matukar jin daɗinsa na Yadda wannan kungiyar ta baiwa Al’umma yankinsa kulawa sannan ya ce zasu bada kowacce irin gudunmawa akan irin wadannnan ayyukan Alkhairi ga kowacce irin kungiya
Sannan kuma mai Unguwar ya bukaci daukacin Al, umma dasu fito nan gaba idan har idan za’a kara irin wannan aikin alkhairin
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa jama’ar da akayiwa wannan gwajin sun nuna matukar jin daɗinsu tare da Yiwa Wadanda sukayi wannan Aiki Fatan alkhairi.
Kungiyar Vision Spring dake zaune a independent road kungiya ce data Shahara wajen aika ce aika ce alkhairi da dama da suka shafi lafiyar jama’a.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
