News
Yan Sanda Sun Kama Angon Bisa Zarginsa Da Hallaka Amaryarsa Har Lahira.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Advertisements
Advertisements
Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta kama wani Ango dan shekara 30, mai sunan Motunrayo Olaniyi, bisa zarginsa da daba wa matarsa mai suna Olajumoke ‘yar shekara 25 daba mata wuka har lahira.
Advertisements
Kakakin rundunar ‘yan sandan,jihar SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Asabar a Jihar.
Advertisements
Advertisements
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1:00 na rana a Amazing Grace Estate, Elepe, a yankin Ikorodu na jihar.
Advertisements
