Connect with us

News

Hukumar FCDA Ta Yi Barazanar Kwace Wasu Filaye Mallakar ‘Ya’yan Buhari Da Wasu Manyan Ƙasa A Najeriya

Published

on

Hukumar FCDA Ta Yi Barazanar Kwace Wasu Filaye Mallakar ‘Ya’yan Buhari Da Wasu Manyan Ƙasa A Najeriya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Hukumar da ke kula da babban birnin tarayya Abuja ta hannun hukumar raya babban birnin tarayya FCDA, ta yi barazanar ga wasu fitattun ‘yan Najeriya da suka haɗa da ‘ya’yan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf da Zahra, da su biya kuɗaɗen da ake bin su na filaye a cikin kwanaki 14, ko kuma su rasa haƙƙin mallakar Filaye.

Advertisement

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa ana sanar da duk wanda abin ya shafa cewa rashin biyan duk wasu kuɗaɗen filaye da kuma caji a cikin lokacin da aka ƙayyade zai haifar da janye tayin mallaka (R-of-O) akan filayen da aka ambata.

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Kwari Dake Kano

Haka zalika Hukumar tà yi  barazanar janye haƙƙin mallakar filayen da fitattun ‘yan Najeriya suka mallaka idan har suka kasa biyan kuɗaɗensu cikin kwanaki 14.

Advertisement

Mutanen da abin ya shafa sun haɗa da:

– Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan shugaban ƙasa Bola Tinubu

Advertisement

– Abbas Tajudeen, kakakin Majalisar wakilai

– George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya

Advertisement

– Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan Harkokin Cikin Gida

– Bukola Saraki, tsohon shugaban Majalisar Dattawa

Advertisement

– Yakubu Dogara, tsohon kakakin Majalisar Wakilai

– Ovie Omo-Agege, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa

Advertisement

– Theodore Orji, Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun, tsoffin gwamnoni

– Dino Melaye, Kabiru Marafa, Stella Oduah, da Ben Bruce, tsaffin ‘yan majalisa

Advertisement

– Adamu Abdullahi, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

– Ameh Ebute, Shugaban Majalisar Dattawan Jamhuriyya ta uku

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending