Connect with us

Politics

Tarihi Ne Ya Maimaita Kansa A Zaɓen Kananan Hukumomin Kano – Kwankwaso

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Jagoran jam’iyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zaɓen ƙananan hukumomin da jam’iyarsa ta gudanar a Kano tarihi ne ya maimaita kansa, “Ba a daki kowa ba, ba a zagi kowa ba, babu wani faɗace-faɗace.”

Kwankwaso ya ce sun san cewa jam’iyun hammaya na iya daukar matakin shari’a shiyasa suma ba su bari an bar su a baya ba kamar yadda BBC HAUSA ta ruwaito.

Advertisement

Duk Da Rashin Wuta, Kamfanin Lantarki Ya Buƙaci A Biya Kuɗin Wuta

“Hukumomin Kano sun san halin wadansu musamman ƴan APC, shiyasa hukumar garzaya kotu saboda ta samu kariya, daman an sanya rai za ayi irin wannan, aka bada hukunci mai ƙwarin gaske wanda ya sanya wa duk wanda zai kawowa dimokradiyya cikasa takunkumi.

Kwankwaso ya ce duk wadanda suke ƙoƙarin rikita jam’iyyar hadin baki ne domin a haifar masu da rudani da rikici cikin jam’iyarsu.

A yau Litinin ne ake sa ran shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano 44, za su shiga ofis domin fara aiki gadan-gadan, bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da su a ranar Lahadi.

Advertisement

An gudanar da bikin rantsarwar a fadar gwamnatin jihar, a gaban manyan ƙusoshin gwamnatin jihar da wakilin sarkin Kano da sarakunan Gaya da Rano da Karaye

Zaɓen jihar Kano na ƙarshen makon jiya, ya zo da matuƙar taƙaddama, inda babbar jam’iyyar adawa a jihar, wato APC ta samo umarnin kotu da ya rusa shugabancin hukumar zaɓen Kano.

Hukumar zaɓen jihar ta bayyana jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar da lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44 da kansiloli 484.

Advertisement

Jami’iyyar APC mai hamayya a jihar ba ta shiga zaɓen ba.

A ranar Talatar ne wata babbar Kotun tarayya a kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda ta rushe shugabancin hukumar zaɓe ta jahar Kano bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar mata na rashin cancantar shugabannin hukumar bisa kasancewarsu ƴan siyasa masu ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP.

Wani ɗan jam’iyyar APC Hon Aminu Tiga da Jam iyyarsa ta APC ne dai suka shigar da ƙara inda suka roƙi kotun da ta rushe shugabannin hukumar zaɓen ta Kano bisa kasancewrsu ƴan jam’iyya mai mulki.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *