News
Hukumar JSC Ta Kano Ta Dauki Matakin Ladabtarwa Kan Ma’aikatan Shari’a Guda Takwas
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Kano a taronta na 76 da ta gudanar a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024, ta dauki matakin ladabtarwa kan ma’aikatan shari’a guda takwas.
Kwamitin korafe-korafen jama’a na hukumar shari’a (JPCC) ya binciki wasu kararraki guda biyu da aka shigar a kan Alkalin Majistare, Nasir Ado, inda bincike ya nuna cewa alkalin ya gudanar da shari’a ba tare da an rubutawa ba, kuma da aka tambaye shi ya yi karya tare da bata bayanan da ke nuna cewa akwai bayanan shari’ar.
Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Irin Dabino Mai Fitowa Sau Biyu A Shekara
Hukumar ta amince da shawarar JPCC, cewa ayyukan da Nasir Ado ya yi na karya da kuma murde bayanan kotun ya zama wani babban rashin da’a don haka aka dawo da shi Zaman ofis daga aikin shari’a.
Biyo bayan karar da kungiyar masu yaki da masu aikata laifuka ta shigar a kan alkalin kotun shari’a Yusuf Kawu, ta tabbatar da cewa Alkali Yusuf Kawu ya yi amfani da matsayinsa na shari’a wajen sakin wani mai laifin da wani Alkali ya yanke masa hukuncin watanni 12 ba tare da zabin tara a gidan gyaran hali ba. Hukumar ta gano abin da Alkalin ya aikata ya sabawa doka kuma ba za a iya kare shi ba, saboda haka an dawo da shi Zaman ofis daga aikin shari’a har illama shaAllah.
Hukumar ta Kuma yi gargadi ga Alkalin Kotun Majistare Mai shari’a Sanusi Usman Atana bayan wasu korafe korafe guda biyu da ake tuhumarsa da su, inda aka same shi da cewa ya dauki nauyin kwato Wadansu wurare a Karar laifi yayin da a korafin na biyu kuma ya bayar da belin wanda ake tuhuma kafin ranar da aka sa a yanke hukunci ba tare da sanar da masu gabatar da kara ba. Don haka, hukumar ta yi kakkausar gargadi ga Sanusi Atana da ya daina wuce gona da iri da kuma kaucewa bin ka’idojin shari’a da aka kafa wajen tafiyar da al’amuran da ke gabansa.
Hukumar da ke kula da harkokin shari’a (JSC) ta bayar da umarnin murabus din dole ga Salisu Adamu Nayola, magatakardan kudi na kotun shari’ar Musulunci ta Kiru, bayan wani bincike da kwamitin kula da korafe-korafen al’amuran shari’a (JPCC) ya karba kan zargin karbar cin hanci da rashawa. Kwamitin na JPCC ya samu takardar koke da ke nuna cewa Adamu Nayola na karbar kudi daga iyalan wadanda suka mutu kafin ya gudanar masu da ayyukansu na rabon gado. Bayan nazari, JPCC ta sami shaidar kai tsaye na waɗannan ayyukan, ciki har da amsawar da Adamu Nayola Yayi na karɓar cin hanci daga masu ƙara da yawa. Bayan bincike an tabbatar da cewa Salisu Nayola yana tare da Alkali Abdulmuminu Nuhu wanda ya nuna halin ko-in-kula da karbar cin hanci da magatakardan ya yi. Hukumar ta amince da shawarar JPCC da Salisu Nayola wanda abin da ya aikata ya zama cin zarafi ga aikinsa a matsayinsa na ma’aikacin shari’a da aka umurce shi da ya ci gaba da ritayar dole, yayin da Alkali Abdulmuminu Nuhu shi Kuma aka umarceshi da ya dawo Zaman ofis daga aikin shari’a na tsawon shekaru biyu. ya Kuma ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar babban magatakarda, kotun daukaka kara ta Sharia.
Hukumar da ke kula da harkokin shari’a (JSC) ta yi gargadi ga Alkali Abubakar Abdullahi na kotun shari’a ta Takai, biyo bayan wani bincike da kwamitin sauraron kararrakin jama’a na shari’a ya gudanar. Kwamitin na JPCC ta samu Alkali Abdullahi ne ya jagoranci wata shari’ar raba kadarorin da ke wajen sa a rukunin gidajen Sabo Garba, Kabuga, da Dorayi Kwanar Makabarta. Hukumar ta amince da shawarar JPCC, inda ta gargadi alkali da ya kiyaye iyakokin yankinsa da kuma kaucewa gudanar da shari’o’in da ba su dace ba.
Bayan binciken da JPCC ta yi kan karar da aka shigar kan Shuaibu Bello, ma’aikacin kotu, wanda aka same shi da aikata almundahana ta hanyar karbar kudi fiye da kima da aka tuhume shi na bude fayil. Kwamitin ya kuma same shi da aikata wani abu da bai dace da ma’aikatan shari’a ba ta hanyar rashin mutunci da rashin mutunta ma’aikacin kotu da yaudarar wanda ya shigar da karar ya sanya hannu kan takardar janye karar. Hukumar ta amince da shawarar kwamitin tare da yin gargadi mai karfi tare da kara dakatar da shi na tsawon watanni hudu ba tare da biyan albashi ba.
Daga karshe biyo bayan binciken da Kwamitin korafe-korafe (JPCC) Yayi a cikin karar da aka shigar kan Shamsu Abbas Magatakardan kotu. Binciken ya nuna magatakardan yayi aikin da ya wuce hurumimsa wajan yanke hukunci ta hanyar sakin wanda ake tuhuma akan beli ba tare da shari’ar taje gaban kowace kotu ba, sannan ya umarci wanda ake tuhuma da ya mayar da ya mayar da Wadansu kuɗade da suka danganci laifin da ake zargi, ayyukan da suka wuce girman aikinsa a matsayin sa na magatakardan kotu. Kwamitin ya gano cewa Abinda ya Aikata babban cin zarafi ne ga aikin magatakardar kotu.
Bayan yi la’akari da shawarwarin JPCC.
da kuma dogon nazari, Hukumar da ke kula da harkokin shari’a,ta Jihar Kano ta bayar da umarnin yin murabus na tilas ga magatakardan kotu Shamsu Abbas.
Hukumar Shari’a ta ci gaba da sadaukar da kai don tabbatar da ganin ma’aikatan shari’a suna gudanar da ayyukansu a cikin iyakokin doka
kuma tare da matuƙar mutunta tsarin shari’a da kuma hukumar za a ci gaba da sanya
takunkumin da ya dace kan duk wani ma’aikaci da ya yi kuskure musamman wadanda ke da nauyin shari’a sannan za a kiyaye da mutunci da kuma hisabi na tsarin shari’a domin Amincewa jama’a .
