News
Sanata Ali Ndume Sanata Da Shehu Sani Sun Yi Sabani A Kan Kudirin Gyaran Dokar Haraji
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sanata Mohammed Ndume (APC-Borno) da Sanata Shehu Sani sun yi sabani a kan kudirin gyaran dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar a gaban majalisar dokokin Najeriya.
Sanata Ndume a cikin wani bayani da ya fitar a Abuja, ya ce dokar ba ta da hurumi a wannan lokacin, musamman lura da halin tsadar rayuwa da al’ummar Najeriya ke ciki.
An Kama Wasu Ƴan TikTok Bisa Zargin Cin Mutuncin Shugaban Kasa
Sai dai tsohon Sanata Shehu Sani na ganin cewa wannan dokar gyaran Harajin zata amfanar da ‘yan Nijeriya, kuma jihohi zasu karbi harajin kayayyaki daga kamfanoni a maimakon su turawa gwamnatin tarayya.