News
Sanata Kawu Ya Yi Barazanar Daukar Matakin Shari’a A Kan Shugaban Jam’iyyar NNPP A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kawu Sumaila ya bai wa shugaban jamiyyarsa ta NNPP a Kano awanni 24 ya janye kalaman da ya yi a kansa ko ya makashi a kotu.
A wata takadda mai ɗauke da sa hannun lauyan Kawu Sumaila, Sunusi Musa SAN ya buƙaci da shugaban NNPP a jihar Kano dake arewacin Najeriya Hashimu Sulaiman Dungurawa ya janye kalaman da yayi masa na zargin cin hanci da maguɗin zabe.
Sanata Ali Ndume Sanata Da Shehu Sani Sun Yi Sabani A Kan Kudirin Gyaran Dokar Haraji
Wannan takadda na zuwa yayin da lamurran siyasa a jihar Kano dake arewacin Najeriya ke ƙara ɗaukar sabon salo tun bayan yawaitar kiraye-kiraye na cewa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafarsa.