Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Kori Ma’aikata Masu Digiri Ɗan Kwatano Da Togo

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Tarayya ta kori ma’aikata masu shaidar kammala karatun digiri daga jami’o’i masu zaman kansu na Jamhuriyar Benin da Togo.

Advertisement

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, Daraktan yaɗa labaran ofishin sakataren gwamnatin Tarayya Segun Imohiosen  ne ya baiyyana cewa matakin ya shafi ma’aikatan da ke aiki tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu.

Tsofaffin Sojoji sun rufe ma’aikatar kudi Ta Abuja Sakamakon Rashin Biyansu Hakkunansu 

A watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin ta sanar da cewa iya jami’o’i 8 na ƙasashen Togo da Jamhuriyar Benin ƙadai ta sahale su bai wa ƴan Najeriya shaidar kammala karatun digiri.

Advertisement

Wannan dai ya biyo binciken ƙwa-ƙwaf da Jaridar DAILY NIGERIAN ta yi wanda ma’aikacinta ya yi basaja da sunan yana neman shaidar karatun digiri , kuma ya samu cikin watanni 2 daga jami’ar Benin, har ma ya yi amfani da shi wajen yin aikin yiwa ƙasa hidima na NYSC.

Lamarin da ya bankaɗo wannan badakala, ya haifar da cece-kuce a sassan Najeriya har ma gwamnatin Tarayya ta haramta halascin shaidar kammala karatu daga jam’o’in Benin da Togo tare da kafa kwamitin bincike kan batun.

Advertisement

Tsohon ministan ilimin a  lokacin, Tahir Mamman ya bayyana cewa sama da ƴan Najeriya 22,500 ne ke da shaidar kammala karatun digiri daga Benin da Togo, kuma an soke halascinsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending