Connect with us

News

Rundunar Sojoji Ta Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindigar Da Ya Kashe Sarkin Gobir

Published

on

Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindigar da ya kashe Sarkin Gobir

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Rundunar sojin Nijeriya ta ɗaya ta cafke ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Baƙo Wurgi wanda aka fi sani da Baka Na Garba a jihar Zamfara.

Ana zargin Wurgi da hannu a kisan Sarkin Gobir na Sabon Birni a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Mohammed Bawa.

HUNTURU: Kasuwar Masu Sana’ar Shayi Kunu Da Awara Da Dangoginsa Ta Bude A Kano

Rundunar ta samu nasarar kama shugaban ‘yan bindingar bayan wani farmaki da ta kai masa a ranar 14 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Shinkafi da ke jihar Zamfara, biyo bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa Wurgi na samun kulawa a wani asibiti da ke yankin, sakamakon raunukan da ya samu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin dabar shi da wata dabar ‘yan bindiga.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa an garzaya da Wurgi zuwa asibiti bayan faɗan da ya ɓarke tsakaninsa da abokan taddancinsa inda ya samu munanan raunin harbin bindinga, wanda hakan ne yasa sojojin suka gano shi tare da kama shi.

Zagazola Makama, ƙwararre a fannin yaƙi da tada ƙayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya tabbatar da wannan samame da aka yi a shafinsa na sada zumunta.

Advertisement

Makama ya bayyana cewa, a yayin samamen, wasu ‘yan bindiga biyu sun yi nasarar tserewa, amma sojoji sun kama wani mutum da ya taimaka wajen jigilar wanda ake zargin ta hanyar amfani da babur mai ƙafa uku.

“Rahotanni sun nuna cewa Wurgi ya taka rawa wajen yin garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe, wanda ya haɗa da neman a biya shi kuɗin fansa da bai yi nasara ba, gami da neman akai masa babura,” inji shi.

“Wurgi mai safarar makamai dake da alaƙa da ƙasashen ƙetare, rahotanni da dama sun sha alaƙanta shi da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji.

“Ana zargin ɗansa, Sani Duna, da ɗaukar Turji saman babur tare da kai shi wuraren da suke ta’addanci, wanda hakan ya ƙara fallasa alaƙa ta ta’addanci tsakanin ‘yan bindingar.” Kamar yadda Makama ya rawaito.

A watan Ogasta, rahotanni da dama sun ruwaito cewa ‘yan ta’addan da suka kashe Alhaji Bawa sun buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 60 da babura biyar domin a sako gawar basaraken gargajiya.

An yi garkuwa da Bawa tare da ɗansa a watan Yuli a Kwanar Maharba yayin da suke kan hanyarsa daga Sokoto zuwa Sabon Birni a jihar Sokoto.

Advertisement

Da farko dai masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su makudan kuɗaɗe har Naira biliyan ɗaya domin a sako su.

Wani Bidiyo mai tayar da hankali da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta ya nuna marigayin basaraken na roƙon a taimaka masa, inda ya bayyana cewa rayuwarsu na cikin haɗari a dajin da ake tsare da shi, sai dai daga bisani an samu labarin ‘yan bindingar sun hallaka shi.

 

 

BLUEPRINT

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending