Connect with us

News

Gwamnan Kaduna Ya Mayarwa Iyalan Abacha Filayen Da El Rufai Ya Kwace

Published

on

Gwamnan Kaduna Ya Mayarwa Iyalan Abacha Filayen Da El Rufai Ya Kwace
Gwamnan Kaduna Uba Sani

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya mayar wa iyalan tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha filayen su guda 2 da tsohon gwamna Nasir El Rufai ya kwace a lokacin mulkinsa.

Daily Trust ta ruwaito cewar lauyan iyalan tsohon shugaban kasar Reuben Atabo ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Ademola Lookman Ya Lashe Kambun Gwarzon Dan Kwallon Afirka Na 2024,

Sanarwar gwamnatin jihar Kaduna da Babban Daraktar ma’aikatar kula da filaye Mustapha Haruna ya gabatar tace Gwamna Sani ya rubutawa iyalan Janar Abacha wasika wanda aka sanya sunan Mohammed Sani Abacha da ta bayyana mayar musu da filayen da kuma gabatar musu da bukatar cewar su je su biya harajin da aka saba karba a hannun su na mallakar filayen.

A shekarar 2022 tsohon gwamnan jihar El Rufai ya gabatar da sanarwa a jarida a ranar 28 ga watan Afrilu wadda ta bayyana kwace filayen tare da soke takardun wadanda aka mallakawa.

Wannan mataki na tsohon gwamnan ya haifar da cece kuce sosai a ciki da wajen jihar Kaduna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending