News
HUNTURU: Kasuwar Masu Sana’ar Shayi Kunu Da Awara Da Dangoginsa Ta Bude A Kano
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Yayin da ake koda sanyi a musamman wasu yankunan Arewacin Najeriya, a jihar Kano masu siyar da awara da soyayyan Dan Kali ne ke caba ciniki.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa mazauna garin da dama suka koma zagayawa teburan masu shayi, da koko da kosai domin dumama jikinsu.
Yadda Yan Daba A Kano Suka Kwace Wayoyin Gwarazan Alqurani Da Zasu Wakilici Jihar A Matakin Kasa.
Haka kuma suma masu soya awara ba a barsu a baya ba.
Wani mai sayar da shayi a unguwar Tarauni Ali Musa ya bayyana cewa, ana samun karuwar bukatar shan shayi mai zafi tun makonni uku da suka gabata.
“Yawancin abokan cinikinmu masu matuka adaidaita sahu ne da yan Acaba, ɗalibai, da ma’aikata. Suna fara zuwa tun da karfe 7:00 na safe su sha shayi sannan su ji dumi kafin su wuce.
Sani Umar dake zaune a unguwar Fage, mai teburin shayi shima ya ce a dan tsakanin nan suna zabga ciniki matuka.
Mudi Saleh, wanda ke sayar da shayi da idomi a Kumbotso, ya ce sai da ya kawo dan uwansa daga kauyen domin ya taimaka wa yawan kwastomomin da yake samu yanzu.
Kofin shayi a rumfarsa yana kan Naira 150 zuwa Naira 300 yayin da farantin indomi ya kan sayar da shi tsakanin Naira 450 zuwa 600, gwargwadon abin da mai bukata ke so.
Aminu Nura, wani mai sayar da shayi da Indomie a Gwale, shi ma ya tabbatar da karuwar kwastomomi.
Ya ce kafin wannan lokaci na hunturu kwastomomi kan koka kan farashin biredi da shi kansa farashin shayi, amma yanzu suna saye da yawa ba tare da koke-koke ba domin a samu saukin jiki kuma a dumama jiki.
Maimuna Yunusa, wacce ke siyar da kosai a kan titin Ahmadu Bello, ta ba da rahoton karuwar kwastomomi.
“A da, yana da wahala in sayar da duk kayana amma yanzu ina sayar da komai da safe,” in ji ta.
