News
Yadda Yan Daba A Kano Suka Kwace Wayoyin Gwarazan Alqurani Da Zasu Wakilici Jihar A Matakin Kasa.
DAGA GWANI IBRAHIM SIRAJ ADHAMA
A satin da ya wuce ne Malam Bukhari Sunusi da Malama Fatima Abubakar su ka yi nasarar zama gwarazan Musabaqar Alqur’ani ta jihar Kano a wannan shekarar a aji na ƙololuwa na Qira’at.
Hakan ya na nufin su ne za su wakilci jihar Kano mai albarka a Musabaqar ƙasa da za a yi a jihar Kebbi tare da sauran ‘yan takara.
Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Naira Tiriliyan 47.9 A Matsayin Kasafin Shekarar 2025
A bisa al’ada duk shekara kafin a tafi ana ba wa ‘yan takara ƙarin horo na musamman wanda ake kira tadreeb kuma ana yinsa ne a Abdullahi Bayero College of Quranic Studies wacce aka fi sani da Kulliyyah dake kan titin Sabuwar Ƙofa.
A jiya Lahadi da misalin ƙarfe biyar na yamma bayan tashin su daga tadreeb waɗannan gwarazan sun fito daga Kulliyyah sun tsallaka titi ɓangaren SAS su na jiran abin hawa kawai sai gungun ‘yan daba sun kusa mutum talatin su ka yo kansu da mugayen makamai abin ba daɗin faɗa.
Nan take su ka fizge jakar Malama Fatima a ciki akwai wayarta da littattafai da wasu abubuwa na kyautuka da aka ba ta a Musabaqar duniya da ta je kwanan nan a Egypt.
Shi ma Malam Bukhari sun ƙwace wayarsa da hularsa mai tsada, ya samu ya tsira da jakarsa.
Haka aka bar su cikin halin razani da ruɗewa.
Babban abin takaici shi ne duk wannan ya faru ne a tsakiyar birnin Kano kuma ido na ganin ido; ko ina ga mutane nan amma ba wanda zai iya yin wani abu har waɗannan ‘yan fashi su ka gama cin kasuwarsu su kai gaba.
Bisa haka ne na ke ganin wajibi ne a ja hankalin mahukunta akan wannan matsalar domin lalacewar ta wuce duk inda ake tunani. Mu ma al’ummar gari ya zama wajibi mu sake nazari akan dabarun kare kai saboda magana ta gaskiya abin ya na nema ya fi ƙarfin gwamnati.
Allah ya mayar musu da mafi alkhairi. Su kuma waɗannan ‘yan ta’adda Allah ya shiryesu, ya kiyaye mu daga sharrinsu. Idan ba masu shiryuwa ba ne Allah ya tona asirinsu, ya ba mu nasara a kansu!
JAR KANWA
