Interview
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadin Raunata Mutum 22 Waɗanda Ke Tattakin Bikin Kirsimeti

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani hatsarin mota ya yi sanadin raunata mutum 22 waɗanda ke tattakin bikin kirsimeti a Gombe, babban birnin jihar Gombe da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da mabiya addinin Kirista ke wani tattaki a cikin garin na Gombe, kamar yadda suka saba a kowace shekara.
Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto
Kakakin rundunar ƴansandan Najeriya a jihar, ASP Buhari Abdullahi ya ce “wata mota ƙirar sharon, maƙare da kayan hatsi ce ta afka cikin masu jerin gwanon ta baya, inda ta buge mutane da dama”.
“Wasu daga cikin waɗanda aka bugen sun samu raunuka har da karaya, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawa.”
ASP Abdullahi ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar ceto direban motar wanda mutane suka hau shi da duka, lamarin da ya so ya haifar da hatsaniya.
Duk da haka, jami’in ya ce masu tattakin sun kammala ziyarar da suka shirya yi a ranar bikin na kirsimeti.
A yau Laraba ne mabiya addinin Kirista a faɗin duniya suka yi bukukuwan Kirsimeti domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Yesu Almasihu.