Connect with us

News

Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Bijiro Da Sauye-sauyen “Da Suka Zama Dole” Domin Gina Ƙasa —Shugaba Tinubu 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Shugaban kasa Bola Ahamd Tinubu,a jawabin sabuwar shekara da ya yiwa yan Najeriya ya yi alkawarin bunkasa noman abinci ,rage hauhawar farashin abinci da magunguna zuwa kashi 15 cikin 100,da kuma karfafa tattalin arziki a shekarar 2025.

Advertisement

A jawabin nasa shugaba, Tinubu ya bayyana alamomin bunkasar tattalin arziki da suka hada da rage farashin man fetur, hauhawar kudaden ajiyar kasashen waje da kuma farfado da darajar Naira, a matsayin alamun ci gaba a shekarar 2024 wanda ya zarto har zuwa 2025.

Shugaba Tinubu Ya Shiga Jerin Shuwagabannin Duniya Da Suka Fi Cin Hanci Da Rashawa A 2024

Ya ce, “Duk da cewa yan kasa sun fuskanci kalubale a shekarar 2024 ina da yakinin cewa sabuwar shekara za ta kawo sauyi.

Advertisement

“Tattalin arziki na karfafa gwiwa ga al’ummarmu. Farashin man fetur ya fara raguwa a hankali, kuma mun sami rarar ciniki a cikin kashi uku a jere.

Kudaden ajiyar kasashen waje ya karu, haka kuma Naira ta kara daraja idan aka kwatanta da dalar Amurka, hakan ya kawo cigaba.”

Advertisement

Haka kuma Shugaba Tinubu ya ce, bunkasar kasuwannin hannayen jari a Najeriya ya samar da arziki na kimanin tiriliyan nairori, inda ya kara da cewa karuwar saka hannun jarin kasashen waje ya samar da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin kasar.

Duk da dai tsadar abinci da magunguna sun kasance babban abin damuwa kuma kalubale ga yan Najeriya a 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending