News
An Samu Bullar Sabuwar Cuta Mai Makamanciyar Covid-19 A Asibitocin Kasar China
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rahotonni sun bayyana cewa an samu bullar sabuwar cuta mai yanayi kamar Covid-19 a asibitocin kasar China.
A Hotunan da suka bayyana a kafafen sada zumunta an ga majinyata sanye da abin rufe fuska a asibitoci daban-daban, da iyaye sun ja dogon layi rike da yayan su suna jiran ganin likita.
Duk da dai har yanzu babu wata sanarwa da ta fito a hukumance game da cutar amma dai ana ganin kamanceceniyar ta da cutar coronavirus da ta data bulla a shekarun baya.
Sai dai Wasu rahotanni sun danganta bullar cutar ga wani kwayar cuta mai suna metapneumovirus (HMPV), kwayar cuta ce da ke illa musamman a sanyi kamar yanda Jaridar THE INDEPENDENT ta ruwaito
Barkewar cutar ta biyo bayan gargadin da cibiyar yaki da cututtuka ta kasar china ta bayar, wadda a baya-bayan nan ta yi gargadi game da karuwar cututtuka masu kama da mura.
Sai Wdaiani rahoto da aka fitar a karshen watan Disamba ya nuna cewa kashi 7.2 cikin 100 na ziyarar marasa lafiya a asibitoci a yankunan arewacin kasar na da nasaba da irin wannan yanayi.
Hakazalika, Kasar Burtaniya ita ma ta fuskanci fama da barkewar cutar mura wadda aka samu marasa lafiya sama da 5,000 a asibiti a karshen watan Disamba.
A cewar BBC, Daraktan Kula da Lafiya kulawar gaggawa, Julian Redhead, ya bayyana ci gaba da yaduwar cututuka nasu kama da mura, COVID-19, RSV, da sauran ƙwayoyin cututtuka.
