News
WAEC Ta Sanar Da Sabon Tsarin Gyara Jarrabawar Da Mutum Ya Fadi Ba Sai Ya Yi Jiran Shekara Daya Ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar WAEC ta sanar da cewa daga yanzu waɗanda suka faɗi wani darasi na jarrabawarsu za su iya sake rubuta shi ba sai sun jira tsawon shekara ɗaya ba.
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar John Kapi ne ya bayyana haka a yayin tattaunawa a kan shirin AM Show na JoyNews a Ghana.
An Samu Bullar Sabuwar Cuta Mai Makamanciyar Covid-19 A Asibitocin Kasar China
Wannan sabon shiri zai bai wa ɗalibai damar sake rubuta jarabawarsu ta Babbar Sakandare ta Afirka ta Yamma (WASSCE) a farkon watan Janairu da Fabrairu 2025.
Wannan babban canji ne idan aka kwatanta da shekarun baya, inda ɗalibai ke jira har sai sawon shekara ɗaya
“Ɗalibai da suka ga sakamakonsu yanzu kuma suka gano suna buƙatar sake rubuta takarda ɗaya ko biyu suna da har zuwa 8 ga Janairu don yin rijista ta yanar gizo ta shafinmu ko a cibiyoyin intanet da WAEC ta amince da su.
“Za a gudanar da jarabawoyin daga ranar 24 ga Janairu zuwa 15 ga Fabrairu 2025,” in ji Kapi
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
