News
Gwamnan Kano Ya Amince Da Murabus Din Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya Da Tabbatar Da Nagartar Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan ma’aikatar bibiya da tabbatar da nagartar aiki Injiniya Mahammad Diggol.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
An dai nada Muhammad Diggol a matsayin kwamishinan sufuri a farkon gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf a shekarar 2023.
Daga baya gwamnan ya mayar da shi ma’aikatar bibiya da tabbatar da nagartar ayyuka, inda ya yi aiki har zuwa wannan lokaci da ya yi murabus.
Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Engr. Diggol bisa hidimarsa da jajircewa gami da sadaukarwar da ya yi a lokacin da yake matsayin dan majalisar zartarwa ta jiha.
A cewar sanarwar, Gwamnan ya kuma mika sakon fatan alheri ga Engr. Diggol a cikin al’amuran rayuwarsa ta gaba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
