News
Muhammad Daga Yobe Ya Lashe Gasar Musabakar QUR’ANI Na Kasa Karo Na 28
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Muhammad Muhammad Sani daga jihar Yobe shine wanda ya lashe gasar musabakar QUR’ANI na kasa karo na 28 wadda aka kammala jiya asabar a jihar Kano.
Rahotanni na nuni da cewa tsawon kwanaki bakwai, mahalarta gasar sun fafata a bangarori daban-daban, suna nuna hazakarsu ta haddacewa, lafazi, da fahimtar Al-Qur’ani.
Gwamnan Kano Ya Amince Da Murabus Din Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya Da Tabbatar Da Nagartar Aiki
Muhammad ya burge alkalan gasar da karatunsa mai kyau ba tare da kuskure ba, tare da nuna cikakken kwarewa a cikin Al-Qur’ani, wanda ya ba shi damar samun maki 99 da ya zama zakara.
An bai wa zakarun dukkan bangarori kyaututtuka daban-daban, ciki har da motoci, kudade, babura, da littattafan addini.
An shirya gasar ne ta hannun Sashen Ilimi na Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir.
Da yake magana a wajen taron, Kwamandan gasar na kasa, Al-Hafiz Aminu Yusuf Nuhu, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da gasar a Jihar Kano cikin shekaru 17.
Nuhu ya yi karin bayani kan tsarin gasar, inda ya ce mahalarta sai sun wuce matakai guda biyar, daga matakin mazabu, karamar hukuma, jiha, sannan su isa matakin kasa.
Ya kara da cewa mahalarta 100,032 daga jihohi 24, tare da mahalarta daga Jamhuriyar Nijar da Ghana, sun shiga gasar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
