Connect with us

News

Hukumar ICPC Ta Gurfanar Da Tsohon Hadimin El-rufa’i A Gaban Kotu Bisa Zargin Almundahana

Published

on

ICPC ta maka tsohon hadimin El Rufa’i kotu bisa zargin almundahana

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon shugaban ma’aikatan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Alhaji Muhammad Bashir Saidu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna.

Advertisement

Haka kuma an gurfanar da wani jami’i a ma’aikatar kuɗi, Ibrahim Muktar, bisa tuhumar da suka shafi zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗe.

Rahotanni na nuni da cewa ana zargin Bashir Saidu, wanda ya taɓa zama Kwamishinan Kudi na Kaduna, da karɓar kuɗaɗe da suka haura Naira miliyan 155 a watan Maris na shekarar 2022, ta hannun wani hadiminsa mai suna Muazu Abdu.

Advertisement

Masu Hidima Ga Kasa Kusha Kuriminku Nan Bada Jimawa Ba Za A Fara Biyan Mafi Karancin Albashi Na N77,000. —Shugaban NYSC

Hukumar ICPC ta bayyana cewa kuɗaɗen sun kasance na wata haramtacciyar hanya kuma hakan ya saɓa wa dokar kuɗaɗe ta shekarar 2022.

A cewar dokar kuɗaɗe ta 2022, duk wanda aka samu da laifin irin wannan yana iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru huɗu zuwa 14, ko tara daidai da sau biyar na kuɗin da aka samu daga laifin, ko ma a haɗa duka biyun. Tuhumar da ake yi wa Saidu da abokin zamansa an gabatar da ita ne a ranar Talata, 7 ga Janairu, 2025, ta hannun lauyan hukumar ICPC, Dakta Osuobeni Ekoi Akponimisingha.

Advertisement

Kotun ta shirya sauraron ƙarar a ranar da za ta bayyana, inda ake sa ran za a ci gaba da bayyana gaskiyar zarge-zargen da ake yi wa waɗanda ake ƙara. Wannan na zuwa ne bayan dogon bincike da aka yi kan zargin almundahana da ya shafi tsohon kwamishinan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending