News
JAMB Ta Bayyana Littafin Da Za A Yi Amfani Da Shi Wajen Darasin Harshen Turanci A 2025

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta bayyana littafin zuben da za a yi amfani da shi wajen amsa tambayoyin harshen Turanci da a kan yi wa ɗalibai na wannan shekara ta 2025.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta shafinta na X a ranar Talata.
Murar Tsuntsaye: An Buƙaci Al’ummar Kano Su Kwantar Da Hankalinsu
Sabon littafin zuben shi ne, ‘The Lekki Headmaster’ wanda Kabir Garba ya rubuta wanda zai maye gurbin littafin ‘Life Changer’ wadda Khadijat Jalli ta rubuta wanda aka yi amfani da shi a bara.
JAMB ta ce nan gaba kaɗan za ta ba da cikakken bayanin yadda rajistar jarrabawar ta bana za ta kasance.
Daga nan hukumar ta buƙaci ɗalibai su cigaba da bibiyar neman ƙarin bayani domin sanin halin da ake ciki.
A duk shekara dai ɗalibai kusan miliyan 1.5 ne rubuta jarrabawar domin neman gurbin karatu a manyan makarantu a Najeriya.
A yayin da hukumar ta ce da sauran lokaci kafin ta bayyana yadda jarrabawar bana za ta kasance, tuni kuma ta fara rantance cibiyoyin rubuta jarrabawar a wani bangare na shirye-shirye gudanarda jarrabawar.
PREMIUM TIMES