Connect with us

News

Majalisa Ta Kara Adadin Kudin Da Hukumar Kwastam Zata Tara A Shekarar 2025

Published

on

Majalisa Ta Kara Adadin Kudin Da Hukumar Kwastam Zata Tara A Shekarar 2025

DAGA MUHAMMAD TUKUNTAWA 

Majalisun dokokin kasa sun kara yawan kudin shigar da hukumar hana fasa kwauri, ta kasa Kwastam, zata tarawa gwamnatin tarayya daga naira triliyan 6.5, zuwa triliyan 12, a wannan shekara ta 2025.

Shugaban kwamitin kudi na majalisar dattawa Sani Musa, da takwaransa na majalisar wakilai James Faleke, ne suka kara adadin kudin shigar da hukumar Kwastam, zata tattara, a ranar talata, lokacin da shugaban hukumar Adewale Adeniyi, ke kare kasafin kudin ma’aikatar sa na 2025.

Ba Zan Taimaki Wannan Gwamnatin Ta Shugaba Tinubu Ba —Sarki Sanusi 

Adeniyi, yace zasu iya tattara naira triliyan 6.5, sakamakon sun tattara triliyan 6.1, a shekarar 2024.

Sai dai majalisar ta mayar masa da martanin cewa kasafin kudin wannan shekara ya wuce ace naira triliyan 6.5, hukumar hana fasa kwaurin zata tattara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending