Connect with us

Entertainment

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta dakatar da amfani da shafukan X da Tiktok

Published

on

An kama wasu ƴan Tiktok bisa zargin cin mutuncin shugaban
Spread the love

DGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ba tare da sanarwa ba, hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun dakatar da amfani da kafafen sada zumunta kamar X da TikTok da kuma amfani da VPN tun a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Ana ganin sun ɗauki matakin ne da niyyar daƙile yaɗuwar labaran ƙarya kan yaƙin da ake yi a gabashin ƙasar, sai dai ƙwararru na gargaɗin hakan zai ta’azzara yaɗa labaran ƙaryan maimakon daƙile shi.

Tallafin Naira Biliyan 150 Ne Yasa Gwamnan Kaduna Ke Goyon Bayan Tinubu — El-Rufa’i

Kafar yaɗa labaran Faransa, RFI ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Fabrairu, alamu na nuna cewa kafafen sada zumunta kamar su X da TikTok sun daina aiki a wasu birane a ƙasar tun ranar 1 ga watan Fabarairu.

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun sanya takunkuman sadarwa tun lokacin da ƴan tawayen M23 suka karɓe iko da birnin Goma a ranar 27 ga watan Janairu.

Kafar yaɗa labarai ta RFI ta ce ta tattauna da mutane a Goma da Lubumbashi da Kalemie da Bukavu da kuma Kinshasa, inda duk suka ce ba sa iya shiga kafafen X da Tiktok a kan wayoyinsu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *