Connect with us

News

Gwanda Ku Nemi A Ci Gaba Da Shirin Haƙo Man fetur A Arewa Maimakon Neman Ƙirƙiro Sabbin Jihohi — Bashir A Bashir

Published

on

IMG 20250207 WA0043

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A lokacin mulkin soja ne ake fafutukar neman jiha, domin kuwa a wancan lokaci mutum guda ne ke da iko. Yanzu kuwa muna cikin tsarin dimokuraɗiyya, wanda dole sai an samu amincewar wasu mutane masu son zuciya kafin a aiwatar da kowanne shiri.

A irin wannan tsarin dimokuraɗiyya da Najeriya ke ciki, batun ƙirƙirar sabbin jihohi har guda 31 abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba.

Sam Ba Ni Da Labari Kan Abin Da Ya Faru A Unguwar Rimin Zakara — Gwamnan Kano 

Saboda haka, muna ganin cewa maimakon a ɓata lokaci da neman sabbin jihohi, ya fi dacewa a mayar da hankali kan dawo da shirin haƙo man fetur a Arewacin Najeriya.

Wannan shiri ne da aka fara a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, amma da zuwan Bola Ahmed Tinubu aka dakatar da shi.

Rashin kishin ƙasa, son zuciya, da taƙama da ‘yancin dimokuraɗiyya ne suka haifar da wannan tattaunawa ta ƙarin jihohi.

Advertisement

Don haka, muna kira da a mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziƙin Arewa ta hanyar farfaɗo da shirin haƙo mai, wanda zai amfanar da al’ummar yankin fiye da kowanne sabon tsari da ba zai yiwu ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending