News
Yadda Mata Ke Saɓa Wa Al’ada Domin Rufa Wa Kansu Asiri Duk Da Ƙalubalen Da Suke Fuskanta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Oluwatosin Ajayi wata mace ce mai gyaran mota da kan fita aiki a kowacce rana da misalin ƙarfe 11 na safe. Kamar kullum dai a watan Nuwambar da PREMIUM TIMES ta gana da ita, ta tuko motarta ce samfurin SUV babban titin Abule-Egba—Abeokuta da ke Legas Lagos inda takan gudanar da sana’arta ta gyaran mota.
Mrs. Ajayi mace ce ‘yar shekara 25 kuma uwa kuma mai shayar da jariri ɗan wata huɗu da haihuwa. Ta iso garajin gyaran motarta cikin farin ciki inda ta tarar da motoci daban-daban da ke jiran ta zo ta gyara su.
‘Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 15 a Kudin Fansar Manomi da Yaransa da Suka Sace
A kusa da garejinta akwai wani ƙwararren mai gyara da ake kira Sunday Osundara amma an fi saninsa da ‘Oga Sunday’ wanda ke aikin gyaran giyar mota, zaune duk hannunsa baƙi ƙirin da baƙin mai.
Zuwan Mrs. Ajayi dai na rayuwa a tsakankanin maza kuma ta aiki ne tare da ƙwararrun masu gyaran mota kamar sun Oga Sunday wanda abun ya zama na daban daga abin da aka saba gani.
Bayan ta nutsa ne ta ɗauko abincinta ta ci, sannan ta shayar da jaririnta tare da canja kayanta ta saka irin na kanikawa mai ɗauke da baƙin mai ta ko’ina.
A yayin da take shirin aiki sai ga wani mai koyon aikin da kayan ɗaukar bidiyo wanda ke ɗaukarta a lokacin da take aiki, ita kuma tana sa wa ne a shafinta na Intagram mai mabiya kusan 100,000, domin yaɗa irin ayyukanta – kasancewarta kallabi tsakanin rawuna.
