Connect with us

Uncategorized

Gidauniyar Attahiru Bafarawa Ta Bada Tallafin Karatu na Shekara Uku ga Dalibai 108 a Jihar Sokoto

Published

on

IMG 20250222 WA0008

 

Daga Mukhtar A. Haliru, Tambuwal – Sokoto

 

A ci gaba da ayyukan jin ƙai na Kwamitin Maida Alkhairi na Gidauniyar Attahiru Bafarawa, an gabatar da tallafin karatu na shekaru uku ga dalibai 108 daga kananan hukumomin jihar Sokoto. Daliban da suka ci gajiyar wannan tallafi sun samu guraben karatu a makarantu biyu na ilimin lafiya da ke cikin garin Sokoto – Gamji College of Nursing Sciences da Al-Huda College of Health Technology.

 

An gudanar da tarurruka a harabar makarantu biyu don kaddamar da bayar da tallafin, inda manyan baki da dama suka halarta. Cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kwamitin, Malam Muhammad Lawal MaiDoki (Sadaukin Sakkwato), Sakataren kwamitin Hon. Sagir Attahiru Bafarawa, shugabannin makarantu, iyayen dalibai, uwayen kasa, jami’an tsaro, da kungiyoyin addinin Musulunci.

Advertisement

 

A yayin taron, an rattaba hannu kan takardun yarjejeniyar tallafi tsakanin kwamitin, makarantu, dalibai da iyayensu, karkashin jagorancin lauya na kwamitin. An bayyana sharuddan tallafin, ciki har da bukatar daliban su dage wajen karatu ba tare da sakaci ba.

 

Kwamitin ya kuma gabatar da takardun shaidar biyan kuɗin makaranta gaba ɗaya na tsawon shekaru uku ga kowane ɗalibi. Wannan tallafi zai ba daliban damar kammala karatunsu cikin kwanciyar hankali.

 

A jawabinsu, shugabannin kwamitin sun bayyana wasu daga cikin ayyukan da suka gabatar har yanzu, ciki har da bada tallafin abinci, duba marasa lafiya kyauta, taimakon masu larurar tabin hankali, da gudanar da wasu ayyuka kamar samar da rijiya, bohol, makarantu da makabartu a sassa daban-daban na jihar.

Advertisement

 

Sun kuma jinjina wa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Attahiru Dalhatu Bafarawa, bisa wannan ƙoƙari na bunkasa ilimi da walwalar al’umma. Har ila yau, sun yaba da haɗin kan gwamnatin jihar Sokoto da Majalisar Mai Martaba Sarkin Musulmi wajen ci gaban ilimi a jihar.

 

Shugabannin makarantu sun nuna godiyarsu bisa wannan tallafi, inda suka tabbatar da cewa irin wannan gudummawa za ta taimaka wajen bunkasa ilimi da inganta rayuwar daliban.

 

A karshe, iyaye da dalibai sun yi addu’ar alheri ga gidauniyar tare da fatan Allah ya saka wa duk masu hannu a wannan aiki da alheri.

Advertisement

 

Adadin Dalibai da Suka Amfana:

 

Gamji College of Nursing Sciences – Dalibai 55

 

Al-Huda College of Health Technology – Dalibai 53

Advertisement

 

 

Wannan tallafi zai bai wa daliban dama su karanci bangarori daban-daban na kiwon lafiya kamar ungozoma da sauran sassa masu muhimmanci, ba kawai a jihar Sokoto ba, har ma da sauran jihohin Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending