Connect with us

News

Gyara APC da Gwamna Uba Sani ya yi ya sa na dawo jam’iyyar – Sanata Shehu Sani

Published

on

Hana 'Yan Majalisa Saka Wani Abu Cikin Kasafin Kudi Shi Ne Kawai Zai mAgance Matsar CusheShehu Sani

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilin komawarsa jam’iyyar APC bayan shekara shida da barinta.

Advertisement

A wata hira da aka yi da shi a shirin Hard Copy na Channels TV a jiya Juma’a, Sani ya ce gyara kuskuren da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya yi, tare da sauyin da Gwamna Uba Sani ya kawo a jam’iyyar APC a Kaduna, ne ya sa ya yanke shawarar dawowa.

Malaman Firamare A Kano Sun Koka Kan Cire Kudi Daga Albashinsu Ba Tare Da Wani Karin Bayani Ba

A watan Oktoba 2018, Sani ya fice daga APC sakamakon rikici da ya biyo bayan zaben fitar da gwani na jam’iyyar. Daga baya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP inda ya nemi kujerar sanata a 2019, amma ya sha kaye a hannun Uba Sani, wanda yanzu shine gwamnan jihar Kaduna.

Advertisement

 

“Wani al’amari ne ya kai mu ga ficewa daga APC a 2018, amma yanzu abubuwa sun canza. Gyaran jam’iyyar da Gwamna Uba Sani ya yi ne ya sa muka yanke shawarar komawa APC,” in ji Shehu Sani.

Advertisement

Ya kara da cewa: “Ni ne daga cikin wadanda suka kafa APC a jihar Kaduna, mun yi aiki tukuru har muka ci zabe a 2015, amma sai muka samu sabani da tsohon gwamna (El-Rufai) wanda ya haddasa rabuwa.”

Sanata Shehu Sani dai na daya daga cikin fitattun ‘yan siyasar da suka sha suka a kan salon mulkin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending