Connect with us

News

Malaman Firamare A Kano Sun Koka Kan Cire Kudi Daga Albashinsu Ba Tare Da Wani Karin Bayani Ba

Published

on

Malaman

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Malaman makarantar firamare a jihar Kano sun koka kan cire kudi daga albashinsu na watan Fabrairu ba tare da wani bayani ko gargadi daga gwamnati ba, inda wasu daga cikinsu suka rasa har naira ₦33,000.

Advertisement

Malaman da abin ya shafa sun bayyana takaicinsu, suna masu  cewa ba a sanar da su ko bayar da wani bayani na hukuma kan dalilin cire kudin ba.

Jaridar KANO TIMES ta ruwaito cewa Musa Ibrahim, malami a wata makarantar gwamnati da ke karamar hukumar Dala, ya ce ya yi matukar mamakin ganin an cire masa ₦18,000 daga albashinsa.

Advertisement

Malaman Firamare A  Kano Sun Yi Koken Cire Kudi Daga Albashinsu Ba Tare Da Bayani Ba

“Na sha wahala wajen aiki duk da matsin tattalin arziki, amma sai na ga an cire mani kudi ba tare da wani bayani ba. Wannan abu ba adalci ba ne,” in ji shi.

Shi ma shugaban kungiyar malamai ta NUT na karamar hukuma, Malam Usman Abdullahi, ya bayyana cewa an cire masa ₦33,000 daga albashinsa.

Advertisement

“A matsayi na na shugaba, ni ma abin ya shafa ne . Wannan abin Allah wadai ne. Muna bukatar bayani daga gwamnati saboda hakan ya jefa malamai da dama cikin kuncin rayuwa,” in ji shi.

Aisha Muhammad, malama daga karamar hukumar Ungogo, ta bayyana cewa an cire mata ₦15,000 daga albashinta.

Advertisement

“Wannan zalunci ne, musamman a irin wannan lokaci da farashin kaya ke tashi. Mun riga mun shiga matsin rayuwa, amma sai kuma gwamnati ta dauki abin da muka wahala muka samu,” ta ce.

Malaman sun bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta yin bayani tare da dawo da kudin da aka cire.

Advertisement

“Ba mu adawa da duk wani caji na doka, amma muna bukatar bayani da gaskiya. Babu wanda ya sanar da mu dalilin cire kudinmu,” in ji Malam Umar Aliyu daga karamar hukumar Kumbotso.

Kokarin jin ta bakin shugaban hukumar SUBEB na jihar Kano, Malam Yusuf Kabir, bai yi nasara ba yayin hada wannan rahoto.

Advertisement

A halin yanzu, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamiti na musamman domin bincikar matsalolin cire albashi da rashin biyan albashi da ke addabar ma’aikatan gwamnati a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana cire kudin a matsayin take hakkin ma’aikata, yana mai alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Advertisement

“Wannan gwamnati ba za ta yarda da zalunci ga ma’aikata ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan abu zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji gwamnan.

Bayan kafa kwamitin, gwamna Yusuf ya dakatar da mukaddashin Shugaban Ma’aikata na jihar, Salisu Mustapha, bisa zargin cire albashi da rashin biyan albashi, tare da nada Umar Jalo a matsayin sabon mukaddashin Shugaban Ma’aikata har sai an kammala bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending