Connect with us

News

Ƴan Ta’adda Sun Kashe Yan Bijilanti 12 Da Yin Garkuwa Da 4 A Zamfara

Published

on

Ƴan ta'adda sun kashe yan Bijilanti 12 da yin garkuwa da 4 a jihar Zamfara.

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

‘Yan bindiga sun kai hari mai muni a kauyen Sabuwar Tunga da ke Adabka, karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara a ranar Talata, inda suka kashe ‘Bijilanti 12 tare da yin garkuwa da mutane hudu.

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun fara kai hari kauyen amma Bijilanti suka fatattake su. Sai dai yayin daBijilanti ke bin su cikin daji, ‘yan bindigar sun sake hadewa tare da yi musu kwanton bauna, wanda ya yi sanadin mutuwar Bijilanti 12.

Manoma Cikin Fargaba Yayin Da Gonakinsu Ke Bushewa Sakamakon Kafewar Dam Din ‘Yan Ganau A Kano

Wani jami’in tsaro da ya tabbatar da lamarin ya ce:

Advertisement

“Mutanen gari sun yi kokari sun fatattaki ‘yan bindigar, amma daga baya sun sake dawowa suka yi waBijilanti kwanton bauna, abin da ya kai ga rasa rayuka.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da harin.

Advertisement

Mazauna yankin sun bukaci hukumomi da su kara daukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending