News
Gwamnatin Kano Ta Bankaɗo Mutane 8,875 Da Ke Zuƙar Inshorar Lafiya Ba Bisa Ka’ida Ba
Gwamnatin Jihar Kano ta gano mutane 8,875 da ke amfana da shirin Inshorar Kiwon Lafiya ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya haddasa asarar har N42,600,000. Wannan badakala ta fito fili ne bayan binciken da hukumar Kano State Contributory Healthcare Management Agency (KSCHMA) ta gudanar.
Binciken ya gano cewa akwai bambanci tsakanin adadin marasa lafiya da ke amfani da shirin da bayanan da aka samu daga asibitoci.
Kotu Ta Yanke Hukuncin Shekaru 95 Kan Dillalan Muggan Ƙwayoyi Da Kuɗinsu Ya Kai Biliyan 4.6
Asibitocin gwamnati ne suka fi samun yawan waɗanda aka ƙirƙira sunayensu, ciki har da Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad – 2,671 Asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase – 2,541 Babban asibitin Waziri Shehu Gidado – 1,126 Babban asibitin Sir Muhammadu Sunusi – 1,023.
Sai kuma Asibitin yara Khalipha Isyaka Rabi’u – 727.
Rahoton binciken ya bayyana cewa waɗanda aka samu da hannu a wannan badakala sun haɗa da masu ritaya da aka ci gaba da lissafa su a matsayin masu amfana.
’Ya’ya da suka haura shekarun da aka ƙayyade ,Mutanen da aka saka a tsarin ba bisa ƙa’ida ba don karɓar ƙarin kuɗaɗen goro
Sakatariyar KSCHMA, Dr. Rahila Aliyu Mukhtar, ta bayyana cewa ana shirin gudanar da bincike na musamman a asibitocin masu zaman kansu da ke cikin tsarin inshorar.
Ayyukan da za a aiwatar sun haɗa da:
Tabbatar da ingancin bayanan masu amfani, Bincike kai-tsaye a asibitoci, Tattaunawa da masu ruwa da tsaki don daƙile matsalar.
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa ta jaddada cewa matakin zai ƙara tabbatar da sahihancin bayanai, hana ɓarnar kuɗi, da kyautata rarraba albarkatu don tabbatar da
ingancin sabis ga waɗanda suka cancanta.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
