News
Kotu Ta Yanke Hukuncin Shekaru 95 Kan Dillalan Muggan Ƙwayoyi Da Kuɗinsu Ya Kai Biliyan 4.6
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos da kuma ta Yola, jihar Adamawa, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 95 a gidan yari kan wasu manyan dillalan muggan ƙwayoyi guda huɗu da aka kama da laifin safarar hodar iblis da darajarta ta kai Naira biliyan 4 da miliyan 600.
Daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin akwai Ogbuji Christian Ifeanyi, wanda jami’an hukumar NDLEA suka kama tun shekarar da ta gabata a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagos, da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kilogram 20.
Sauran waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (Don) da kuma Zidon Zurga.
Kotun ta kuma umarci ƙwace motoci biyu da aka yi amfani da su wajen safarar ƙwayoyin, tare da biyan tarar Naira miliyan 25.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa, ya yaba da wannan hukunci da ya ce babban ci gaba ne a yaki da fataucin muggan ƙwayoyi a ƙasar nan.
Sanarwar hukumar na ƙara nuna aniyar NDLEA na ci gaba da tunkarar masu aikata wannan laifi da duk mai hannu a safarar muggan ƙwayoyi a Najeriya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
