News
Layin wutar lantarki na Najeriya ya samu tsaiko
Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya sun ce sun fuskanci matsala a yau Juma’a daga babban layin wutar, lamarin da ya jawo yankuna da dama cikin duhu.
Kamfanin Kedco da ke bai wa jihar Kano da makwabtanta wuta, ya nemi afuwar kwastomominsa, yana mai cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, wanda ya hana su ci gaba da ba da wuta.
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Daukar Ma’aikatan Lafiya 774 Karkashin Shirin ‘Health Fellows’
Haka zalika, kamfanin Ikeja Electric mai rarraba wuta a Legas ya fitar da irin wannan sanarwa, amma dukkan kamfanonin sun ƙi bayyana musabbabin matsalar.
A halin da ake ciki, hukumar rarraba wutar lantarki ta ƙasa, Transmission Company of Nigeria (TCN), ba ta ce uffan ba kan lamarin da ya shafi wasu sassa na Abuja da sauran wurare.
Akasari, irin wannan matsala kan faru ne idan babban layin lantarki na ƙasa ya samu tangarɗa, wanda ke ci gaba da zama ƙalubale ga tsarin wutar lantarkina ƙasar.
