News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Daukar Ma’aikatan Lafiya 774 Karkashin Shirin ‘Health Fellows’
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya 774 karkashin shirin ‘National Health Fellows’, wani shiri na musamman da ma’aikatar lafiya ta ƙaddamar domin bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya a Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da shirin a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, tare da halartar manyan jami’an gwamnati, abokan haɗin guiwa da sarakunan gargajiya, ciki har da Olu na Warri, Ogiame Atuwatse III.
Rundunar Anty Snatching Phone Ta Kama Barayi Biyu Da Ake Zargi Da Ƙwace Wayoyi A Kano
Sabbin ma’aikatan da aka ɗauka an zaɓo su ne daga kowacce ƙaramar hukuma 774 ta ƙasar nan, bayan tantance mutane 360,000 da suka nemi aikin. Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate, ya bayyana cewa zaɓen an yi shi ne bisa cancanta ba tare da nuna bambanci ba.
“Ina farin cikin ganin yadda matasanmu suka nuna ƙwazo da kwarewa a wannan shiri. Wannan shiri na kawo sauyi ne da zai taimaka wajen inganta lafiyar al’umma,” in ji Farfesa Pate.
Shugaba Tinubu ya yaba da yadda aka gudanar da shirin, yana mai cewa:
> “Wannan shiri na ‘Health Fellows’ na daga cikin shirye-shiryen da gwamnatina ke da su domin bai wa matasa damar bada gudunmowa ga cigaban Najeriya. Ku ne ginshiƙin hangen nesanmu na samar da ƙwararru a fannin lafiya.
Ya kuma buƙaci sabbin ma’aikatan da su yi amfani da wannan dama don hidimtawa al’umma da kuma zama manyan shugabanni a fannin lafiya nan gaba.
Ministan kuɗi da tattalin arziƙi, Wale Edun, da ministan matasa, Ayodele Olawande, sun yaba da shirin tare da ƙarfafa sabbin ma’aikatan su jajirce wajen hidimtawa al’umma.
Sarakunan gargajiya, ciki har da Olu na Warri, sun bayyana shirin a matsayin wata dama ta musamman da za ta kawo sauyi a fannin kiwon lafiya.
Shirin ‘Health Fellows’ wani gagarumin mataki ne na gwamnatin Tinubu na bunƙasa fannin lafiya da kuma bai wa matasa damar bada gudunmowa ga cigaban ƙasa. Sabbin ma’aikatan da aka ɗauka ana sa ran za su taka rawa wajen samar da sauyi mai ɗorewa a ɓangaren kiwon lafiya a Najeriya.
