News
Kotu Ta Dakatar Da INEC Daga Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
Kotun Tarayya da ke Lokoja ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙata da ke da alaƙa da shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa.
Kotun ta kuma hana ma’aikatan INEC, wakilansu, ko duk wani mai hannu a lamarin daga karɓar sunayen ƙarya ko gudanar da taruka kan batun, har sai an yanke hukunci na ƙarshe. Wannan umarni ya biyo bayan ƙorafin wasu ‘yan yankin Kogi ta Tsakiya, da suka nemi kariya daga abin da suka kira yunƙurin tauye haƙƙinsu.
Ayyuka Takwas Masu Tarin Lada A Kwanaki 10 Na Ƙarshen Watan Ramadan.
Lauyan masu ƙorafin, Smart Nwachimere, ya wakilci masu ƙarar a gaban kotu, inda aka ɗage shari’a zuwa 6 ga Mayu, 2025, domin ci gaba da sauraron karar.
A martaninsu, wata ƙungiya mai suna Action Collective ta yaba da hukuncin kotun, inda shugabansu, Dr. Onimisi Ibrahim, ya ce matakin ya nuna rashin amincewa da wasu ‘yan siyasa da ke ƙoƙarin cire Senata Natasha daga kujerarta.
